Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 28:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Adalci ne zai zama igiyar gwajin tushen ginin, aminci kuma zai zama shacin dirin ginin.Hadirin ƙanƙara zai share dukan ƙarairayin da kuke dogara gare su, rigyawa za ta hallakar da zaman lafiyarku.”

18. Alkawarin da kuka ƙulla da mutuwa ya tashi, yarjejeniyar da kuka yi da lahira, an soke ta. Sa'ad da masifa ta auko za a hallaka ku.

19. Za ta yi ta auko muku a kai a kai kowace safiya. Tilas ku sha ta dare da rana. Kowane sabon jawabin da zai zo muku daga wurin Allah, zai kawo muku sabuwar razana!

20. Za ku zama kamar mutumin da ya zama abin karin magana, wanda ya yi ƙoƙari ya kwanta a gajeren gado, ya kuma rufa da ɗan siririn bargo.

21. Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.

22. Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.

23. Ku kasa kunne ga abin da nake cewa, ku mai da hankali ga abin da nake faɗa muku.

Karanta cikakken babi Ish 28