Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 28:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mulkin Isra'ila ya ƙare, darajarsa tana dushewa kamar rawanin furanni a kan shugabanninsa da suka bugu da giya. Sun bulbula turare a kawunansu na girmankai, amma ga su nan a kwance bugaggu.

2. Ubangiji yana da wani ƙaƙƙarfa mai iko a shirye don ya fāɗa musu da yaƙi. Zai zo kamar hadirin ƙanƙara, kamar kwararowar ruwan sama, kamar kuma rigyawa mai kirmewa wadda ta shafe ƙasa.

3. Za a tattake girmankan bugaggun shugabannin nan.

4. Darajan nan mai dushewa ta shugabanni masu girmankai za ta shuɗe kamar 'ya'yan ɓaure, nunan fari, da aka tsinke aka cinye nan da nan da nunarsu.

5. Rana tana zuwa da Ubangiji Mai Runduna zai zama kamar rawanin furanni mai daraja ga jama'arsa da suka ragu.

6. Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.

7. Har da annabawa da firistoci, tangaɗi suke yi, mashaya ne. Sun sha ruwan inabi da barasa da yawa, suna ta tuntuɓe barkatai. Annabawan sun bugu ƙwarai, har ba su iya fahimtar wahayin da Allah ya aiko musu ba, firistoci su ma sun bugu, har sun kāsa yanke shari'un da aka kawo musu.

8. Duk sun cika teburorin da suke zaune da amai, ba inda ba su amaye ba.

9. Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!

10. Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”

11. Idan ba za ku saurare ni ba, to, Allah zai yi amfani da baƙi masu magana da harshen da ba ku sani ba, su koya muku darasi.

Karanta cikakken babi Ish 28