Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 27:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.

4. Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus.

5. Amma idan maƙiyan jama'ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”

6. A wannan rana jama'ar Isra'ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. 'Ya'yan da suka yi za su cika duniya.

7. Ubangiji bai hukunta Isra'ila da tsanani kamar yadda ya yi wa maƙiyanta ba, ba za su yi hasarar mutane da yawa ba.

8. Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.

9. Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.

10. Birni mai garu ya zama kufai. An bar shi kamar jejin da ba kowa ciki. Ya zama wurin kiwon shanu, inda za su huta su yi kiwo.

11. Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.

Karanta cikakken babi Ish 27