Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 27:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da yake cikin teku.

2. A wannan rana Ubangiji zai yi magana a kan kyakkyawar gonar inabinsa,

3. ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.

4. Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus.

5. Amma idan maƙiyan jama'ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”

6. A wannan rana jama'ar Isra'ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. 'Ya'yan da suka yi za su cika duniya.

7. Ubangiji bai hukunta Isra'ila da tsanani kamar yadda ya yi wa maƙiyanta ba, ba za su yi hasarar mutane da yawa ba.

8. Ubangiji ya hukunta jama'arsa da ya sa aka kai su baƙuwar ƙasa. Ya sa iskar gabas mai ƙarfin gaske ta tafi da su.

Karanta cikakken babi Ish 27