Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 26:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya.Sa'ad da kake yi wa duniya da jama'arta shari'aDukansu za su san yadda adalci yake.

10. Ko da yake kana yi wa mugaye alheri,Duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba.Har a nan ma, a ƙasar adalai,Suna ta aikata kuskure,Sun ƙi ganin girmanka.

11. Maƙiyanka ba su san za ka hukunta su ba.Ya Ubangiji, ka kunyatar da su, ka sa su sha wahala,Wato su sha wahalar hukuncin da ka shirya.Ka nuna musu yawan ƙaunar da kake yi wa jama'arka.

12. Kai za ka wadata mu, ya Ubangiji,Duk abin da muka iya yi daga gare ka ne.

13. Ya Ubangiji Allahnmu, waɗansu sun mallake mu,Amma kai kaɗai ne Ubangijinmu.

14. Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba,Kurwarsu ba za ta tashi ba,Domin ka hukunta su, ka hallaka su.Ba wanda zai ƙara tunawa da su.

15. Ya Ubangiji, ka sa al'ummarmu ta yi ƙarfi,Ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe,Wannan kuwa ya sa ana girmama ka.

16. Ka hukunta jama'arka, ya Ubangiji,A cikin azaba sun yi addu'a gare ka.

Karanta cikakken babi Ish 26