Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 26:17-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kai ne, ya Ubangiji, ka sa muka yi kuka,Kamar macen da take naƙuda tana kuka da azaba.

18. Muna shan azaba da wahala,Amma ba abin da muka haifa.Ba mu ciwo wa ƙasarmu nasara ba,Ba abin da muka kammala!

19. Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa!Jikunansu za su sāke rayuwa!Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansuZa su farka, su yi waƙa don farin ciki!Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya,Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.

20. Jama'ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.

21. Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.

Karanta cikakken babi Ish 26