Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 21:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”

10. Ya jama'ata, an buga ku kamar yadda ake bugun alkama a masussuka. Amma yanzu na kawo muku albishir wanda na ji daga wurin Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila.

11. Wannan shi ne jawabi a kan Edom.Wani daga Edom ya kira ni ya ce, “Ya mai tsaro, gari ya kusa wayewa? Ka gaya mini har sai yaushe zai waye?”

12. Sai na amsa na ce, “Gari zai waye, amma za a sāke yin dare! Idan kana so ka sāke yin tambaya, sai ka sāke zuwa, ka tambaya.”

13. Wannan shi ne jawabi a kan Arabiya.Ya ku jama'ar Dedan, waɗanda ayarorinku suka yi zango a ƙasar Arabiya wadda take faƙo,

14. ku ba jama'a waɗanda suka zo gare ku masu jin ƙishi ruwa su sha. Ya ku jama'ar ƙasar Tema, ku ba 'yan gudun hijira abinci.

15. Mutane suna gudu don su tsere wa takuban da za su kashe su, da bakkunan da za su harbe su, su kuma tsere wa dukan hatsarorin yaƙi.

16. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Saura shekara ɗaya tak girman kabilar Kedar zai ƙare.

17. Jarumawan Kedar su ne maharba, amma sai kaɗan za su ragu daga cikinsu, ni, Ubangiji Allah na Isra'ila, na faɗa.”

Karanta cikakken babi Ish 21