Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 21:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan Babila.Kamar yadda guguwa take tasowa daga hamada, haka masifa za ta auko daga wata ƙasa mai razanarwa.

2. Na ga wahayi na waɗansu mugayen abubuwa, wato na cin amana da hallakarwa.Rundunar sojojin Elam, ku kama yaƙi! Rundunar sojojin Mediya ku kewaye birane da yaƙi. Allah zai kawar da wahalar da Babila ta haddasa.

3. Abin da na gani, da abin da na ji a wahayin, ya razanar da ni, ya sa ni cikin azaba kamar ta mace mai naƙuda.

4. Kaina ya yi yum, ina ta rawar jiki saboda tsoro. Ina ta marmarin maraice ya yi, amma bai kawo mini kome ba, sai razana.

5. A wahayin na ga an shirya biki, an shisshimfiɗa darduma inda waɗanda aka gayyata za su zauna. Suna ci suna sha. Farat ɗaya sai aka ji umarni cewa, “Jarumawa! Ku shirya garkuwoyinku.”

6. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sa mai tsaro, ka faɗa masa ya riƙa ba da labarin abin da ya gani.

Karanta cikakken babi Ish 21