Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 20:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bisa ga umarnin Sargon, Sarkin Assuriya, sai sarkin yaƙin Assuriya ya fāɗa wa Ashdod, birnin Filistiyawa, da yaƙi.

2. A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.

3. Sa'ad da aka ci Ashdod, sai Ubangiji ya ce, “Bawana Ishaya ya yi ta yawo tsira, ba kuma takalmi a ƙafarsa har shekara uku. Wannan ita ce alamar abin da zai faru a ƙasa Masar da Habasha.

Karanta cikakken babi Ish 20