Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 19:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabi a kan Masar.Ubangiji yana zuwa Masar a kan girjije a sukwane. Gumakan Masarawa za su yi rawar jiki a gabansa, zuciyar Masarawa za ta karai.

2. Ubangiji ya ce, “Zan ta da hargitsi a yi yaƙin basasa a Masar, ɗan'uwa ya yi gāba da ɗan'uwa, maƙwabci kuma gaba da maƙwabci. Biranen da suke hamayya za su yi faɗa da juna, sarakunan da suke hamayya kuma za su yi faɗa saboda neman iko.

3. Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.

4. Zan ba da Masarawa a hannun azzalumi a hannun mugun sarki kuma da zai mallake su. Ni, Ubangiji Mai Runduna, na faɗi wannan.”

5. Ruwan Kogin Nilu zai ƙafe, a hankali kogin zai bushe.

6. Mazaunan kogin za su ji wari sa'ad da yake ƙafewa a hankali. Iwa da jema za su bushe.

7. Dukan amfanin gonakin da aka shuka a gaɓar Kogin Nilu za su bushe, iska ta fyauce su.

8. Duk wanda sana'arsa ta kama kifi ce a Kogin Nilu zai yi ƙugi ya yi kuka, gama ƙugiyoyinsa da tarunansa za su zama marasa amfani.

9. Waɗanda suke yin tufafin lilin za su fid da zuciya,

10. shugabanni da ma'aikata za su karai su kuma damu.

Karanta cikakken babi Ish 19