Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 15:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Mutanen Heshbon da na Eleyale suka yi kuka da ƙarfi, har ana iya jin kukansu daga Yahaza. Har mayaƙa ma sun yi rawar jiki, zuciyarsu ta karai.

5. Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki.

6. Rafin Nimra ya ƙafe, ciyawar da take gefensa ta bushe, ba sauran wani ɗanyen abu.

Karanta cikakken babi Ish 15