Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 14:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji zai sāke yi wa jama'arsa Isra'ila jinƙai, ya zaɓe su su zama nasa. Zai sāke sa su zauna a ƙasarsu, baƙi ma za su zo su zauna tare da su.

2. Al'ummai da yawa za su taimaki jama'ar Isra'ila su koma ƙasarsu wadda Ubangiji ya ba su. A can sauran al'umma za su yi wa Isra'ila hidima kamar bayi. Waɗanda suka kama Isra'ilawa a dā yanzu Isra'ilawa za su kama su. Jama'ar Isra'ila za ta mallaki waɗanda suka taɓa zaluntarsu.

3. Ubangiji Allah kuwa zai sawwaƙe wa jama'ar Isra'ila azaba da wahala da suke sha, daga kuma aikin da aka tilasta su su yi.

4. Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a.Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba!

5. Ubangiji ya ƙare mulkin mugun,

6. wanda yake zaluntar jama'a a husace, bai taɓa daina tsananta wa al'ummai ba, wanda ya ci da yaƙi.

7. Yanzu magana ta ƙare, duniya duka tana jin daɗin hutawa da salama. Kowa na ta raira waƙar murna.

8. Itatuwan fir da itatuwan al'ul na Lebanon suna murna da faɗuwar sarkin! Ba wanda zai tasar musu da sara!

9. “Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu.

10. Dukansu suka yi kira gare shi, suka ce, ‘Ashe, kai ma rarrauna ne kamarmu! Ka zama ɗaya daga cikinmu.

11. Dā ana ɗaukaka ka da kaɗe-kaɗen garaya, amma yanzu ga ka a lahira! Kana kwance a kan tsutsotsi. Kana rufe da tsutsotsi!’ ”

12. Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.

13. Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.

14. Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka.

15. Amma a maimakon haka an saukar da kai a sashe mafi zurfi a lahira.

Karanta cikakken babi Ish 14