Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 10:27-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. A lokacin nan zan 'yantar da ku daga mulkin Assuriya, karkiyarsu ba za ta ƙara zama kaya mai nauyi a wuyanku ba.”

28. Magabta suna cikin Ayiyat! Sun bi ta Migron! Sun bar kayayyakinsu a Mikmash!

29. Sun ƙetare hanya suka kwana a Geba! Mutanen Rama suka firgita. Mutanen da suke cikin Gibeya, garin sarki Saul, sun gudu.

30. Ku yi ihu, ku mutanen Gallim! Ku kasa kunne, ku mutanen Layish! Ku amsa, ku mutanen Anatot!

31. Jama'ar Madmena da na Gebim suna gudu su tsira da rayukansu.

32. Yau abokan gāba suna cikin Nob, daga can suke nuna wa Dutsen Sihiyona yatsa, wato wanda yake cikin Urushalima.

33. Ubangiji Mai Runduna zai sa su ragargaje har ƙasa, kamar rassan da aka sassare daga itace. Masu girmankai da manyansu za a datse su ƙasa, a ƙasƙantar da su.

34. Ubangiji zai sassare su har ƙasa kamar yadda ake sassare itatuwa da gatari a tsakiyar kurmi, kamar yadda itatuwa mafi kyau na Lebanon za su fāɗi.

Karanta cikakken babi Ish 10