Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 1:16-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ku yi wanka sarai. Ku daina aikata dukan wannan mugun abu da na ga kuna aikatawa. I, ku daina aikata mugunta.

17. Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”

18. Ubangiji ya ce, “Yanzu fa, bari mu daidaita al'amarinmu. Duk kun yi ja wur da zunubi, amma zan wanke ku, ku yi fari fat kamar auduga. Zai yiwu zunubinku ya sa ku zama ja wur, amma za ku yi fari fat kamar farin ulu.

19. Idan za ku yi mini biyayya kaɗai za ku ci kyawawan abubuwan da ƙasa take bayarwa.

20. Amma idan kuka ƙi, kuka raina ni, mutuwa ce ƙaddararku. Ni Ubangiji na faɗi wannan.”

21. Birnin da yake dā mai aminci ne, yanzu ya zama kamar karuwa! Dā adalai a can suke zaune, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai.

22. Ya Urushalima, dā kamar azurfa kike, amma yanzu ba ki da amfani, dā kamar kyakkyawan ruwan inabi kike, amma yanzu baƙin ruwa ne kaɗai.

23. Shugabanninku 'yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari'a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.

24. Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.

25. Zan hukunta ku. Zan tace ku kamar yadda ake tace ƙarfe, in kawar da dukan ƙazantarku.

26. Zan ba ku shugabanni da mashawarta kamar waɗanda kuke da su dā can. Sa'an nan za a ce da Urushalima adala, amintaccen birni.”

27. Gama Ubangiji mai adalci ne, zai ceci Urushalima da dukan wanda ya tuba a can.

28. Amma zai ragargaza dukan wanda ya yi zunubi, ya tayar gāba da shi, zai kashe duk wanda ya rabu da shi.

Karanta cikakken babi Ish 1