Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Ish 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Abin da yake rubuce a littafin nan, jawabi ne a kan Yahuza da Urushalima, wanda Allah ya bayyana wa Ishaya ɗan Amoz a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.

2. Ubangiji ya ce, “Duniya da sararin sama, ku kasa kunne ga abin da ni, Ubangiji, nake cewa! 'Ya'yan da na goya sun tayar mini.

3. Shanu sun san ubangijinsu, jakai sun san wurin da ubangijinsu yake ba su abinci. Amma wannan ya fi abin da jama'ata Isra'ila suka sani. Ba su gane ba ko kaɗan.”

4. An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.

5. Me ya sa kuke ta tayarwa? Kuna so a ƙara muku hukunci ne? Ya Isra'ila, kanki duka rauni ne, zuciyarki da kwanyarki suna ciwo.

6. Daga kanki har zuwa ƙafafunki, ba inda yake da lafiya a jikinki. Raunuka da ƙujewa da manyan gyambuna sun rufe jikinki, ba a tsabtace raunukanki an ɗaure ba. Ba a yi musu magani ba.

Karanta cikakken babi Ish 1