Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 9:20-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Irmiya ya ce,“Ya ku mata, ku ji maganarUbangiji,Ku kasa kunne ga maganar da yafaɗa,Ku koya wa 'ya'yanku mata kukanmakoki,Kowacce ta koya wa maƙwabciyartawaƙar makoki,

21. Gama mutuwa ta shiga tagoginmu,Ta shiga cikin fādodinmu,Ta karkashe yara a tituna,Ta kuma karkashe samari a dandali.

22. Ubangiji ya ce mini,‘Ka yi magana, cewa gawawwakinmutane za su fāɗi tuliKamar juji a saura,Kamar dammunan da masu girbisuka ɗaura,Ba wanda zai tattara su.’ ”

23. Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.

24. Amma bari wanda zai yi fariya, ya yi fariya a kan cewa ya fahimce ni, ya kuma san ni. Ni ne Ubangiji mai yin alheri, da gaskiya, da adalci a duniya, gama ina murna da waɗannan abubuwa, ni Ubangiji na faɗa.”

25. Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa sa'ad da zan hukunta dukan waɗanda aka yi musu kaciya,

26. da Masar, da Yahuza, da Edom, da 'ya'yan Ammon, maza, da na Mowab, da dukan waɗanda suke zaune a hamada, da waɗanda suke yi wa kansu sanƙo, gama dukan al'umman nan marasa kaciya ne, dukan jama'ar Isra'ila kuma marasa kaciya ne a zuci.”

Karanta cikakken babi Irm 9