Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 9:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ma kaina ruwa ne kundum,Idanuna kuma maɓuɓɓuga ne,Da sai in yi ta kuka dare da rana,Saboda an kashe jama'ata!

2. Da ma ina da wurin da zan fake ahamada,Da sai in rabu da mutanena, in tafican!Gama dukansu mazinata ne,Ƙungiyar mutane maciya amana.

3. Ubangiji ya ce,“Sun tanƙwasa harshensu kamarbaka,Ƙarya ce take rinjayar gaskiya aƙasar.Suna ta cin gaba da aikata mugunta,Ba su kuwa san ni ba.

4. “Bari kowane mutum ya yi hankalida maƙwabcinsa,Kada kuma ya amince da kowaneirin ɗan'uwa,Gama kowane ɗan'uwa munafukine,Kowane maƙwabci kuma mai kushene.

5. Kowane mutum yana ruɗinmaƙwabcinsa da abokinsa,Ba mai faɗar gaskiya,Sun koya wa harshensu faɗarƙarya.Suna aikata laifi,Sun rafke, sun kasa tuba.

6. Suna ƙara zalunci a kan zalunci,Yaudara a kan yaudara,Sun ƙi sanina,” in ji Ubangiji.

7. Saboda haka, Ubangiji MaiRunduna, ya faɗa cewa,“Zan tsabtace su, in gwada su,Gama me zan yi kuma sabodajama'ata?

Karanta cikakken babi Irm 9