Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 7:25-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Tun daga ran da kakanninku suka fito ƙasar Masar, har zuwa yau na yi ta aika musu da dukan bayina annabawa kowace rana.

26. Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.

27. “Saboda haka za ka faɗa musu waɗannan abubuwa duka, amma ba za su ji ka ba. Za ka kira su, amma ba za su amsa ba.

28. Za ka faɗa musu ka ce, wannan ita ce al'ummar da ba ta yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnta ba, ba ta karɓi horo ba. Gaskiya kuma ta ƙare sam, ba ta a bakinsu.

29. “Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi 'yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa.

30. Ni Ubangiji, na faɗa, cewa mutanen Yahuza sun yi mugun abu a gabana. Suna ajiye gumakansu a Haikalina, sun ƙazantar da shi.

31. A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata.

32. Domin haka, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa lokacin da ba za a ƙara faɗar Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a kira shi Kwarin Kisa, gama za a binne mutane a Tofet domin ba sauran wuri a ko'ina.

33. Gawawwakin mutanen nan za su zama abincin tsuntsaye da na namomin jeji, ba wanda zai kore su.

Karanta cikakken babi Irm 7