Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 7:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2. “Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada!

3. Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ku gyara hanyoyinku da ayyukanku, ni kuwa zan ƙyale ku, ku zauna a wannan wuri.

4. Kada ku amince da maganganun nan na ruɗarwa, cewa wannan shi ne Haikalin Ubangiji. Wannan shi ne Haikalin Ubangiji, wannan shi ne Haikalin Ubangiji!

5. “ ‘Idan dai kun gyara hanyoyinku, da ayyukanku bisa kan gaskiya, idan da gaskiya kuke aikata adalci ga junanku,

6. idan ba ku tsananta wa baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, idan ba ku zubar da jinin marar laifi a wannan wuri ba, idan kuma ba ku bi abin da zai cuce ku ba, wato gumaka,

7. sa'an nan zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasa wadda tuni na ba kakanninku har abada.

8. “ ‘Ga shi, kun amince da maganganu na ruɗami, marasa amfani.

9. Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?

Karanta cikakken babi Irm 7