Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 6:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ya ku mutanen Biliyaminu, kugudu neman mafaka,Daga cikin Urushalima!Ku busa ƙaho a Tekowa,Ku ba da alama a Bet-akkerem,Gama masifa da babbar halaka sunfito daga arewa.

2. Ya Sihiyona, ke kyakkyawarmakiyaya ce, zan hallaka abin dakika hahhaifa.

3. Makiyaya da garkunansu za su zowurinki,Za su kafa alfarwansu kewaye da ke,Kowa zai yi kiwo a makiyayarki.

4. Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa matada yaƙi!Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakarrana!’Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, garana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.

5. Mu tashi mu fāɗa mata da dare,Mu lalatar da fādodinta.’ ”

6. Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ku sassare itatuwanta,Ku tula ƙasa kewaye daUrushalima,Dole in hukunta wannan birnisaboda ba kome cikinsa saizalunci,

7. Kamar yadda rijiya take da ruwagarau,Haka Urushalima take damuguntarta,Ana jin labarin kama-karya da nahallakarwa a cikinta,Kullum akwai cuce-cuce, da raunukaa gabana,

8. Ku ji faɗaka, ya ku mutanenUrushalima,Don kada a raba ni da ku,Don kada in maishe ku kufai,Ƙasar da ba mazauna ciki.”

9. Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Za a kalace ringin Isra'ila sarai,kamar yadda ake wa inabi,Ka miƙa hannunka a kan rassantakamar mai tsinkar 'ya'yaninabi.”

10. Da wa zan yi magana don in faɗakarda shi, don su ji?Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, suji,Ga shi, maganar Ubangiji kuwa tazama abin ba'a a gare su,Ba su marmarinta.

11-12. Don haka ina cike da fushinUbangijiNa gaji da kannewa.Ubangiji ya ce,“Zan kwararo fushi kan yara da suke atiti.Da kuma kan tattaruwar samari.Za a ɗauke mata da miji duka biyu,Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufatukub-tukub.Za a ba waɗansu gidajensu, dagonakinsu, da matansu,Gama zan nuna ikona in hukuntamazaunan ƙasar.

13. Gama daga ƙaraminsu zuwa babba,Kowannensu yana haɗama ya ciƙazamar riba,Har annabawa da firistoci,Kowannensu ya shiga aikata rashingaskiya.

Karanta cikakken babi Irm 6