Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 50:26-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Ku zo, ku fāɗa mata daga kowanesashi.Ku buɗe rumbunanta,Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi,Ku hallakar da ita ɗungum,Kada wani abu nata ya ragu.

27. Ku kashe dukan bijimanta, a kai sumayanka!Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare,Lokacin hukuncinsu ya yi.

28. Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasarBabila,Don su faɗa cikin Sihiyona,Sakayyar Ubangiji Allahnmu dominHaikalinsa.

29. “Ku kirawo 'yan baka, dukanwaɗanda sukan ja baka, su faɗawa Babila.Ku kafa sansani kewaye da ita, kadaku bar kowa ya tsira.Ku sāka mata bisa ga dukanayyukanta, gama ta raina UbangijiMai Tsarki na Isra'ila.

30. Domin haka samarinta za su fāɗi atituna.Za a hallaka sojojinta duka a wannanrana,Ni Ubangiji na faɗa.

31. “Ga shi, ina gāba da ke, ke Babila,mai girmankai.Gama ranar da zan hukunta ki, ta zo,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

32. Mai girmankai za ta yi tuntuɓe tafāɗi,Ba kuwa wanda zai tashe ta,Zan ƙone garuruwanta da wuta,Zan kuma hallaka dukan abin da yakekewaye da ita.

33. “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce,An danne mutanen Isra'ila da naYahuza,Duk waɗanda suka kama su bayi sunriƙe su da ƙarfi.Sun ƙi su sake su.

34. Mai fansarsu mai ƙarfi ne,Ubangiji Mai Runduna ne sunansa.Hakika zai tsaya musu don ya kawowa duniya salama,Amma zai kawo wa mazaunan Babilafitina.

35. Ni Ubangiji na ce,Akwai takobi a kan Kaldiyawa,Da a kan mazaunan Babila,Da a kan ma'aikatanta da masuhikimarta,

36. Akwai takobi a kan masu sihiriDon su zama wawaye.Akwai takobi a kan jarumawantaDon a hallaka su.

37. Akwai takobi a kan mahayandawakanta, da a kan karusanta,Da a kan sojojin da ta yi ijara da suDon su zama kamar mata,Akwai takobi a kan dukan dukiyartadomin a washe ta.

38. Fari zai sa ruwanta ya ƙafe,Gama ƙasa tana cike da gumakawaɗanda suka ɗauke hankalinmutane.

39. “Domin haka namomin jeji da diloliza su zauna a Babila,Haka kuma jiminai.Ba za a ƙara samun mazauna acikinta ba har dukan zamanai.

40. Abin da ya faru da Saduma daGwamrata,Da biranen da suke kewaye da su,Shi ne zai faru da Babila.Ba mutumin da zai zauna cikinta.

41. “Ga mutane suna zuwa daga arewa,Babbar al'umma da sarakunaSuna tahowa daga wurare masu nisana duniya.

Karanta cikakken babi Irm 50