Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 50:25-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ubangiji ya buɗe taskarmakamansa,Ya fito da makaman hasalarsa,Gama Ubangiji Allah Mai Rundunayana da aikin da zai yi a ƙasarKaldiyawa.

26. Ku zo, ku fāɗa mata daga kowanesashi.Ku buɗe rumbunanta,Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi,Ku hallakar da ita ɗungum,Kada wani abu nata ya ragu.

27. Ku kashe dukan bijimanta, a kai sumayanka!Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare,Lokacin hukuncinsu ya yi.

28. Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasarBabila,Don su faɗa cikin Sihiyona,Sakayyar Ubangiji Allahnmu dominHaikalinsa.

29. “Ku kirawo 'yan baka, dukanwaɗanda sukan ja baka, su faɗawa Babila.Ku kafa sansani kewaye da ita, kadaku bar kowa ya tsira.Ku sāka mata bisa ga dukanayyukanta, gama ta raina UbangijiMai Tsarki na Isra'ila.

30. Domin haka samarinta za su fāɗi atituna.Za a hallaka sojojinta duka a wannanrana,Ni Ubangiji na faɗa.

31. “Ga shi, ina gāba da ke, ke Babila,mai girmankai.Gama ranar da zan hukunta ki, ta zo,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

Karanta cikakken babi Irm 50