Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:27-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”

28. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,“Ku tashi zuwa Kedar,Ku hallaka mutanen gabas.

29. Za a kwashe alfarwansu dagarkunansu,Da labulan alfarwansu, da dukankayansu.Za a kuma tafi da raƙumansu,Za a gaya musu cewa, ‘Razana takewaye ku!’

30. “Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwanesa,Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji nafaɗa,Gama Nebukadnezzar, SarkinBabila, ya shirya mukumaƙarƙashiya,Ya ƙulla mugun nufi game da ku.

31. Ku tashi ku fāɗa wa al'ummar da takezama lami lafiya,Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare,Suna zama su kaɗai.

Karanta cikakken babi Irm 49