Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:25-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ƙaƙa aka manta da sanannen birni,Birnin da take cike da murna?

26. A waccan rana samarinta za su fāɗi adandalinta.Za a hallaka sojojinta duka,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

27. Zan kuma sa wuta a garun Dimashƙu,Za ta kuwa cinye fādodinBen-hadad.”

28. Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan Kedar da sarakunan Hazor, waɗanda sarki Nebukadnezzar ya ci da yaƙi,“Ku tashi zuwa Kedar,Ku hallaka mutanen gabas.

29. Za a kwashe alfarwansu dagarkunansu,Da labulan alfarwansu, da dukankayansu.Za a kuma tafi da raƙumansu,Za a gaya musu cewa, ‘Razana takewaye ku!’

30. “Ku mazaunan Hazor, ku gudu zuwanesa,Ku ɓuya cikin zurfafa, ni Ubangiji nafaɗa,Gama Nebukadnezzar, SarkinBabila, ya shirya mukumaƙarƙashiya,Ya ƙulla mugun nufi game da ku.

31. Ku tashi ku fāɗa wa al'ummar da takezama lami lafiya,Waɗanda ba su da ƙofofi ko ƙyamare,Suna zama su kaɗai.

32. “Za a washe raƙumansu dagarkunan shanunsu ganima,Zan watsar da masu yin kwaskwasko'ina,Zan kuma kawo musu masifu dagakowace fuska,Ni Ubangiji na faɗa.

33. Hazor za ta zama kufai har abada,wurin zaman diloli,Ba wanda zai zauna a ciki, ba wandakuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”

34. Maganar da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Elam a farkon sarautar Zadakiya Sarkin Yahuza.

35. Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Zan karya bakan Elam, indaƙarfinta yake.

36. Zan sa iska ta hura a kan Elam dagakusurwoyi huɗu na samaniya.Za ta watsar da mutane ko'ina,Har ba ƙasar da za a rasa mutuminElam a ciki.

37. Zan sa mutanen Elam su ji tsoronmaƙiyansu waɗanda suke nemanransu.Da zafin fushina zan kawo musumasifa,In sa a runtume su da takobi,Har in ƙare su duka,Ni Ubangiji na faɗa.

38. Zan kafa gadon sarautata a Elam,Zan hallaka sarkinta dashugabanninta.

Karanta cikakken babi Irm 49