Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 49:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne abin da Ubangiji ya faɗa akan Ammonawa,“Isra'ila ba shi da 'ya'ya ne?Ko kuwa ba shi da māgada ne?Me ya sa waɗanda suke bautar Milkomsuka mallaki inda Gad take zama,Suka zauna a garuruwanta?

2. Domin haka lokaci yana zuwa,Sa'ad da zan sa mutanen garinRabba ta Ammon su ji busaryaƙi.Rabba za ta zama kufai,Za a ƙone ƙauyukanta da wuta,Sa'an nan Isra'ila zai mallakiwaɗanda suka mallake shi.Ni Ubangiji na faɗa.

3. “Ki yi kuka, ya Heshbon, gama Ai tazama kufai!Ku yi kuka, ku mutanen Rabba, kusa tufafin makoki.Ku yi gudu, kuna kai da kawowa acikin garuka,Gama za a kai Milkom bauta tare dafiristocinsa da wakilansa.

4. Me ya sa kuke taƙama daƙarfinku,Ƙarfinku da yake ƙarewa, ku mutanemarasa aminci?Kun dogara ga dukiyarku,Kuna cewa, ‘Wane ne zai iya gāba damu?’

5. Ga shi, zan kawo muku razana dagawaɗanda suke kewaye da ku,Za a kore ku, kowane mutum zaikama gabansa,Ba wanda zai tattara 'yan gudunhijira.Ni Ubangiji Allah Mai Rundunana faɗa.

6. “Amma daga baya zan saAmmonawa su wadata kuma,Ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Irm 49