Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 48:18-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.

19. Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.

20. An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.

21. “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22. da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23. da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

24. da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.

25. An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

26. “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.

27. Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.

28. “Ku mazaunan Mowab, ku bargaruruwanku,Ku tafi, ku zauna a kogwanni,Ku zama kamar kurciya wadda takeyin sheƙarta a bakin kwazazzabo.

29. Mun ji labarin girmankan Mowab,da ɗaukaka kanta,Da alfarmarta, da izgilinta,Tana da girmankai ƙwarai.

30. Ni Ubangiji na san Mowab tana dagirmankai,Alfarmarta ta banza ce,Ayyukanta kuma na banza ne.

31. Don haka zan yi kuka sabodaMowab duka,Zan kuma yi baƙin ciki sabodamutanen Kir-heres.

32. Zan yi kuka saboda kurangar inabinSibmaFiye da yadda zan yi kuka sabodamutanen Yazar.Rassanku sun haye teku har sun kaiYazar,Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan'ya'yan itatuwanku da damunaDa kan amfanin inabinku.

Karanta cikakken babi Irm 48