Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 48:15-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Mai hallaka Mowab da garuruwantaya taho,Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sungangara mayanka,Ni sarki, mai suna Ubangiji MaiRunduna, na faɗa.

16. Masifar Mowab ta kusato,Halakarta kuma tana gaggabtowa.

17. “Ku yi makoki dominta, ku da kukekewaye da ita,Dukanku da kuka san sunanta, kuce,‘Ƙaƙa sandan sarauta mai ikoDa sanda mai daraja ya karye?’

18. Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.

19. Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.

20. An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.

21. “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22. da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23. da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

24. da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.

25. An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

26. “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.

27. Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.

28. “Ku mazaunan Mowab, ku bargaruruwanku,Ku tafi, ku zauna a kogwanni,Ku zama kamar kurciya wadda takeyin sheƙarta a bakin kwazazzabo.

29. Mun ji labarin girmankan Mowab,da ɗaukaka kanta,Da alfarmarta, da izgilinta,Tana da girmankai ƙwarai.

Karanta cikakken babi Irm 48