Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 48:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ubangiji ya ce, “Domin haka kwanaki suna zuwa, sa'ad da zai aika da mutane su tuntsurar da tuluna, su zubar da ruwan inabi, su farfasa tulunanta.

13. Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.

14. “Don me kake cewa,‘Mu jarumawa ne, mayaƙan gaske?’

15. Mai hallaka Mowab da garuruwantaya taho,Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sungangara mayanka,Ni sarki, mai suna Ubangiji MaiRunduna, na faɗa.

16. Masifar Mowab ta kusato,Halakarta kuma tana gaggabtowa.

17. “Ku yi makoki dominta, ku da kukekewaye da ita,Dukanku da kuka san sunanta, kuce,‘Ƙaƙa sandan sarauta mai ikoDa sanda mai daraja ya karye?’

18. Ku da kuke zaune a Dibon,Ku sauka daga wurin zamanku maidaraja,Ku zauna a busasshiyar ƙasa,Gama mai hallaka Mowab ya zo yayi gab da ku.Ya riga ya rushe kagararku.

19. Ku mazaunan Arower,Ku tsaya a kan hanya, ku jira,Ku tambayi wanda yake guduDa wanda yake tserewa,Abin da ya faru.

20. An kunyatar da Mowab, ta rushe.Ku yi kuka dominta,Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab tahalaka.

21. “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22. da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23. da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

24. da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.

25. An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

Karanta cikakken babi Irm 48