Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 44:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan dukan Yahudawan da suke zaune a ƙasar Masar, a garin Migdol, da Tafanes, da Memfis, da dukan ƙasar Fatros, ya ce,

2. “Ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, na ce, ku da kanku kun ga masifar da na aukar wa Urushalima, da dukan garuruwan Yahuza. Yanzu sun zama kufai, ba wanda yake zaune a cikinsu,

3. domin mutanen da suke cikinsu sun aikata mugayen abubuwa da suka tsokane ni. Sun miƙa wa gumaka hadayu, suka kuma bauta musu, ko da yake su, ko ku, ko kakanninku, ba ku san su ba.

4. Na yi ta aika muku da dukan bayina annabawa waɗanda suka faɗa muku kada ku aikata wannan mugun abin banƙyama.

5. Amma ba su kasa kunne ba, ba su kuwa ji ba, da za su juyo daga mugayen ayyukansu na miƙa wa gumaka hadayu.

6. Saboda haka fushina ya yi zafi a kan garuruwan Yahuza da titunan Urushalima, don haka a yanzu sun lalace, suka zama kufai.

7. “Yanzu, ni Ubangiji Allah Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ina tambaya, me ya sa kuke jawo wa kanku wannan babbar masifa, kuna so ku hallakar da mata da maza, yara da jarirai daga cikin Yahuza, har a rasa wanda zai wanzu?

8. Me ya sa kuke tsokanata da ayyukan hannuwanku, kuna miƙa wa gumaka hadayu a ƙasar Masar inda kuka zo don ku zauna? Yin haka zai sa a hallaka ku, ku zama abin la'ana da zargi a cikin dukan ƙasashen duniya.

9. Ko kun manta da mugayen ayyukan kakanninku, da na sarakunan Yahuza da na matansu, da naku, da na matanku, waɗanda suka aikata a ƙasar Yahuza da kan titunan Urushalima?

10. Amma har wa yau ba ku ƙasƙantar da kanku ba, ba ku ji tsorona ba, ba ku kuwa kiyaye dokokina da umarnaina ba, waɗanda na ba ku ku da kakanninku.

11. “Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan aukar muku da masifa, in hallaka mutanen Yahuza duka.

12. Sauran mutanen Yahuza kuwa waɗanda suka ragu, waɗanda suke niyyar zuwa ƙasar Masar da zama, zan sa dukansu su halaka a can. Takobi da yunwa za su kashe dukansu a Masar, da yaro da babba. Za su zama abin la'antawa, da abin tausayi, da abin zargi, da abin kunya.

13. Zan hukunta dukan waɗanda suke zaune a Masar kamar yadda na hukunta wa Urushalima da takobi, da yunwa, da annoba.

14. Ba waɗansu daga cikin mutanen Yahuza da suka ragu, waɗanda suka zo Masar da zama, da za su tsere ko su rayu. Ba wani daga cikinsu da zai koma Yahuza inda suke marmarin komawa da zama, ba wanda zai koma, sai dai 'yan gudun hijira.”

15. Sai dukan mazan da suka sani matansu sun miƙa wa gumaka hadayu, da dukan matan da suke tsaye a wurin, da dukan Yahudawan da suke zaune a Fatros, babban taron jama'a, suka ce wa Irmiya,

16. “Ba za mu kasa kunne ga jawabin da kake yi mana da sunan Ubangiji ba!

17. Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.

18. Amma tun da muka daina miƙa wa sarauniyar sama hadayu, da hadayu na sha, ba mu da kome, sai dai takobi da yunwa suke kashe mu.”

Karanta cikakken babi Irm 44