Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 4:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Har yaushe zan yi ta ganin tuta,In yi ta jin amon ƙaho?

22. Ubangiji ya ce,“Mutanena wawaye ne,Ba su san ni ba,Yara ne dakikai,Ba su da ganewa.Suna gwanance da aikin mugunta,Amma ba su san yadda za su yinagarta ba.”

23. Da na duba duniya sai na ga kufai cekawai ba kome,Na kuma dubi sammai sai na ga bahaske.

24. Da na duba duwatsu, sai na ga sunamakyarkyata,Dukan tuddai kuma suna rawar jiki,su yi gaba su yi baya.

25. Na duba sai na ga ba ko mutumɗaya,Dukan tsuntsaye kuma sun tsere.

26. Na duba, sai na ga ƙasa mai dausayita zama hamada,An mai da dukan biranentakangwayeA gaban Ubangiji saboda zafinfushinsa.

27. Gama Ubangiji ya ce, “Ƙasar duka za ta zama kufai, amma duk da haka, ba wannan ne zai zama ƙarshenta na har abada ba.

28. Duniya za ta yi makoki sabodawannan,Sammai za su duhunta,Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufain yi,Ba zan ji tausayi ba,Ba zan kuwa fāsa ba.”

Karanta cikakken babi Irm 4