Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 4:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama'ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba!

12. Wannan iska da za ta zo daga wurin Ubangiji, tana da mafificin ƙarfi. Yanzu fa zan yanke hukunci a kansu.”

13. Duba, ga abokin gāba yana zuwakamar gizagizai,Karusan yaƙinsa suna kama daguguwa,Dawakansa sun fi gaggafa sauri.Kaitonmu, mun shiga uku!

14. Ya Urushalima, ki wanke muguntadaga zuciyarki,Domin a cece ki,Har yaushe mugayen tunaninki za suyi ta zama a cikinki?

15. Gama wata murya daga Dan tafaɗa,Ta kuma yi shelar masifar da za tafito daga duwatsun Ifraimu.

16. “A faɗakar da al'ummai, yana zuwa,A faɗa wa Urushalima cewa,‘Masu kawo mata yaƙi suna zuwadaga ƙasa mai nisa,Suna yi wa biranen Yahuza ihu.

17. Za su kewaye Yahuza kamar masutsaron saura,Saboda ta tayar wa Ubangiji.’ NiUbangiji na faɗa.

18. “Al'amuranki da ayyukanki sukajawo miki wannan halaka,Tana da ɗaci kuwa,Ta soki har can cikin zuciyarki.”

19. Azaba! Ba zan iya daurewa da azababa!Zuciyata! Gabana yana faɗuwa daƙarfi,Ba zan iya yin shiru ba,Gama na ji amon ƙaho da hargowaryaƙi.

20. Bala'i a kan bala'i,Ƙasa duka ta zama kufai,An lalatar da alfarwaina, ba zato batsammani,Labulena kuwa farat ɗaya.

21. Har yaushe zan yi ta ganin tuta,In yi ta jin amon ƙaho?

Karanta cikakken babi Irm 4