Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 39:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya yi wa Nebuzaradan shugaban matsara umarni a kan Irmiya ya ce,

12. “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”

13. Sai Nebuzaradan shugaban matsara, da Nebushazban, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan shugabannin Sarkin Babila,

14. suka aika aka kawo Irmiya daga gidan waƙafi, suka ba da Irmiya amana ga Gedaliya, ɗan Ahikam ɗan Shafan, don ya kai shi gida. Da haka Irmiya ya zauna tare da mutane.

15. Ubangiji ya yi magana da Irmiya a lokacin da aka kulle shi a gidan waƙafi, ya ce,

16. “Ka tafi ka faɗa wa Ebedmelek mutumin Habasha, cewa Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Zan sa masifa, ba alheri ba, ta auko wa wannan birni. Wannan kuwa zai faru a kan idanunka a wannan rana.

17. Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba.

Karanta cikakken babi Irm 39