Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 37:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zadakiya ɗan Yosiya, wanda Nebukadnezzar, Sarkin Babila ya naɗa Sarkin Yahuza, ya yi mulki a maimakon Yekoniya ɗan Yehoyakim.

2. Amma shi da barorinsa, da mutanen ƙasar, ba wanda ya kasa kunne ga maganar Ubangiji wadda ya yi musu ta bakin annabi Irmiya.

3. Sai sarki Zadakiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya, da Zafaniya firist, ɗan Ma'aseya, a wurin annabi Irmiya cewa, “Ka yi addu'a ga Ubangiji Allah dominmu.”

4. A lokacin nan Irmiya yana kai da kawowa a cikin mutane, gama ba a tsare shi a kurkuku ba tukuna.

5. Rundunar sojojin Fir'auna kuwa ta taho daga Masar, amma da Kaldiyawa waɗanda suka kewaye Urushalima da yaƙi suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.

6. Sai Ubangiji ya yi magana da annabi Irmiya, ya ce,

7. “Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na ce ka faɗa wa Sarkin Yahuza wanda ya aiko ka ka tambaye ni, ka faɗa masa cewa, ‘Rundunar sojojin Fir'auna, wadda ta kawo maka gudunmawa tana gab da juyawa zuwa ƙasarta a Masar.

Karanta cikakken babi Irm 37