Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 33:2-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce,

3. “Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”

4. Gama haka Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, a kan gidajen da suke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi.

5. “Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu.

6. Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya.

7. Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā.

8. Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini.

9. Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al'umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”

10. Haka Ubangiji ya faɗa, “A wannan wuri da ka ce ya zama kufai, ba mutum ko dabba, wato a biranen Yahuza da titunan Urushalima, inda ba kowa, ba mutum ko dabba a ciki,

11. za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa,‘Ku yi godiya ga Ubangiji MaiRunduna,Gama Ubangiji nagari ne,Gama madawwamiyar ƙaunarsatabbatacciya ce.’Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”

12. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Wannan wuri wanda yake kufai, inda ba mutum ko dabba, da cikin dukan biranensa, zai sāke zama makiyaya, inda masu kiwo za su zauna da garkunansu.

13. A garuruwan ƙasar tuddai, da na kwaruruka, da na Negeb, da na ƙasar Biliyaminu, da na wuraren da suke kewaye da Urushalima, da na Yahuza, garkuna za su sāke bi ta ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,” in ji Ubangiji.

14. “Ga shi, kwanaki suna zuwa sa'ad da zan cika alkawarin da na yi wa mutanen Isra'ila da na Yahuza.

Karanta cikakken babi Irm 33