Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 33:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya sāke yin magana da Irmiya sa'ad da yake a kulle a gidan waƙafi.

2. Ubangiji wanda ya halitta duniya, ya siffata ta, ya kafa ta, sunansa Ubangiji, ya ce,

3. “Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”

4. Gama haka Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, a kan gidajen da suke a wannan birni, da gidajen sarakunan Yahuza, waɗanda aka rurrushe domin a yi wa garukan jigo saboda mahaurai da suka kewaye birni, da kuma saboda yaƙi.

5. “Sa'ad da ake zuwa yaƙi da Kaldiyawa gidaje za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata, gama na ɓoye wa wannan birni zatina saboda dukan muguntarsu.

6. Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya.

7. Zan kuma mayar wa mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila da arzikinsu, in sāke kafa su kamar yadda suke a dā.

8. Zan shafe dukan laifin da suka yi mini, in kuma gafarta musu dukan zunubansu da tayarwar da suka yi mini.

Karanta cikakken babi Irm 33