Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 31:28-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

28. Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa.

29. A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa,‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masutsami,Haƙoran 'ya'ya suka mutu’ ba.

30. Amma kowa zai mutu sabodazunubin kansa,Wanda ya ci inabi masu tsami,Shi ne haƙoransa za su mutu.”

31. Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza.

32. Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa.

33. Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.

34. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”

35. Haka Ubangiji ya ce,Shi wanda ya ba da rana ta haskakayini,Ya sa wata da taurari su ba da haskeda dare,Shi ne yakan dama teku, ya saraƙumanta su yi ruri,Sunansa Ubangiji Mai Runduna.

36. “Idan dai wannan kafaffiyar ka'idata daina aiki a gabana,Ni Ubangiji na faɗa,To, ashe, zuriyar Isra'ila za ta dainazama al'umma a gabana ke nanhar abada.

37. Idan a iya auna sammai a kuma iyabincike tushen duniya a ƙarƙas,To, ashe, zan watsar da dukanzuriyar Isra'ila ke nan sabodadukan abin da suka yi,Ni Ubangiji na faɗa.

38. “Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa.

39. Sa'an nan ma'aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa'an nan ya nausa zuwa Gowa.

40. Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”

Karanta cikakken babi Irm 31