Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 31:18-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. “Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yanacewa,‘Ka hore ni, na kuwa horu,Kamar ɗan maraƙin da ba shi dahoro,Ka komo da ni don in zama kamaryadda nake a dā,Gama kai ne Ubangiji Allahna.

19. Gama na tuba saboda na rabu dakai,Bayan da aka ganar da ni, sai nasunkuyar da kai,Kunya ta kama ni, na gigice,Domin ina ɗauke da wulakancinƙuruciyata.’

20. Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccenɗana ba ne?Ashe, shi ba ɗan gaban goshina bane?A duk lokacin da na ambace shi akan muguntarsaNakan tuna da shi da ƙauna.Saboda na ƙwallafa zuciyata akansa,Hakika zan yi masa jinƙai, niUbangiji na faɗa.”

21. Ki kafa wa kanki alamun hanya,Ki kafa wa kanki shaidu,Ki lura da gwadabe da kyau,Hanyar da kin bi, kin tafi.Ya budurwa Isra'ila, ki komo,Komo zuwa biranen nan naki.

22. Har yaushe za ki yi ta shakka,Ya ke 'yar marar bangaskiya?Gama Ubangiji ya halitta sabon abua duniya,Mace ce za ta kāre namiji.”

23. Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu.‘Ubangiji ya sa maka albarka,Ya wurin zaman adalci,Ya tsattsarkan tudu!’

24. Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu.

25. Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

26. Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.”

27. “Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza.

Karanta cikakken babi Irm 31