Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 31:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Ku ji maganar Ubangiji,Ya ku al'ummai,Ku yi shelarsa har a ƙasashen da sukenesa, na gāɓar teku.Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsaIsra'ila zai tattaro ta,Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayiyakan kiyaye garkensa.’

11. Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu.Ya fanshe shi daga hannuwanwaɗanda suka fi ƙarfinsa.

12. Za su zo su raira waƙa da ƙarfi,A bisa ƙwanƙolin Sihiyona,Za su yi annuri saboda alherinUbangiji,Saboda hatsi, da ruwan inabi, damai,Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu.Rayuwarsu za ta zama kamarlambu,Ba za su ƙara yin yaushi ba.

13. Sa'an nan 'yan mata za su yi rawada farin ciki,Samari da tsofaffi za su yi murna.Zan mai da makokinsu ya zamamurna,Zan ta'azantar da su, in ba su farinciki maimakon baƙin ciki.

Karanta cikakken babi Irm 31