Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 29:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ga maganar wasiƙar da annabi Irmiya ya aika daga Urushalima zuwa ga dattawa, da firistoci, da annabawa, da dukan mutanen da Nebukadnezzar ya kwaso daga Urushalima zuwa Babila. (

2. Ya rubuta wannan bayan tashin sarki Yekoniya, da uwa tasa, da bābāni, da sarakunan Yahuza, da na Urushalima, da gwanayen aikin hannu, da maƙera daga Urushalima.)

3. Ya aika da wasiƙar ta hannun Elasa ɗan Shafan, da Gemariya ɗan Hilkiya waɗanda Zadakiya Sarkin Yahuza ya aika zuwa Babila, wurin Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Ga abin da wasiƙar ta ce.

4. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce wa dukan waɗanda aka kai bauta, wato waɗanda ya aika da su bauta daga Urushalima zuwa Babila.

5. ‘Ku gina gidaje, ku zauna a ciki, ku dasa gonaki, ku ci amfaninsu.

6. Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.

7. Amma ku nemi zaman lafiyar birni inda na sa aka kai ku zaman talala, ku yi addu'a ga Ubangiji saboda birnin, gama zaman lafiyar birnin shi ne naku zaman lafiyar.’

8. Gama haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa. ‘Kada ku yarda annabawanku da malamanku na duba waɗanda suke tare da ku su ruɗe ku, kada ku kasa kunne ga mafarkansu.

9. Gama annabcin da suke yi muku da sunana, ƙarya ne, ni ban aike su ba.’

10. “Ubangiji ya ce, ‘Sa'ad da kuka cika shekara saba'in a Babila, zan ziyarce ku, zan kuwa cika muku alkawarina. Zan komo da ku zuwa wannan wuri.

11. Gama na san irin shirin da na yi muku, ni Ubangiji na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya.

Karanta cikakken babi Irm 29