Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 25:30-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. “Kai Irmiya kuma sai ka yi annabcin dukan waɗannan magana gāba da su, ka faɗa musu cewa,‘Ubangiji zai yi ruri daga Sama,Zai yi magana daga wurin zamansamai tsarki,Zai yi wa garkensa ruri da ƙarfiƙwarai,Zai yi ihu kamar masu matse'ya'yan inabi,Zai yi gāba da dukan mazaunanduniya.

31. Za a ji hayaniya har iyakar duniya,Gama Ubangiji yana da ƙara gameda al'ummai,Zai shiga hukunta wa dukan 'yanadam,Zai kashe mugaye da takobi,Ubangiji ya faɗa.’ ”

32. Haka Ubangiji Mai Runduna ya ce,“Ga masifa tana tahowa dagaal'umma zuwa al'umma,Hadiri kuma yana tasowa dagadukan manisantan wurare naduniya.

33. Waɗanda Ubangiji ya kashe awannan rana,Za su zama daga wannan bangonduniya zuwa wancan.Ba za a yi makoki dominsu ba,Ba kuwa za a tattara gawawwakinsua binne ba.Za su zama taki ga ƙasa.

34. “Ku yi makoki, ku yi kuka, kumakiyaya,Ku yi ta birgima a cikin toka kuiyayengijin garke,Gama ranar da za a yanka ku daranar da za a warwatsa ku ta zo,Za ku fāɗi kamar zaɓaɓɓen kasko.

Karanta cikakken babi Irm 25