Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 25:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. a shekarar ce, annabi Irmiya ya yi wa dukan mutanen Yahuza da dukan mazaunan Urushalima magana cewa,

3. “Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.

4. Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da yake Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa,

5. yana cewa, ‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada.

6. Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.’

7. Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

8. “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,

9. zan aiko kabilai daga arewa da bawana Nebukadnezzar, Sarkin Babila. Zan kawo su, su yi yaƙi da ƙasan nan da mazaunanta, da dukan al'umman da take kewaya da ita. Zan hallaka su sarai, in sa su zama abin ƙyama, da abin raini, da abin zargi har abada.

10. Banda haka zan kawar da muryar sowa da ta farin ciki, da ta ango da ta amarya, da amon dutsen niƙa daga gare su. Zan kashe hasken fitilunsu.

11. Ƙasar duka za ta zama kufai marar amfani, waɗannan al'ummai za su bauta wa Sarkin Babila har shekara saba'in.

Karanta cikakken babi Irm 25