Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 25:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A shekara ta huɗu ta mulkin Yehoyakim ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Ubangiji ya yi wa Irmiya magana a kan dukan mutanen Yahuza. A shekarar da Nebukadnezzar ya ci sarautar Babila,

2. a shekarar ce, annabi Irmiya ya yi wa dukan mutanen Yahuza da dukan mazaunan Urushalima magana cewa,

3. “Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.

4. Ba ku saurara ba, ba ku kasa kunne don ku ji ba, ko da yake Ubangiji ya yi ta aiko muku da dukan bayinsa annabawa,

5. yana cewa, ‘Sai kowane ɗayanku ya juyo daga mugun halinsa da mugayen ayyukansa don ya zauna a ƙasar da Ubangiji ya ba ku, ku da kakanninku tun daga zamanin dā har abada.

6. Kada ku bi gumaka, ku bauta musu, ku yi musu sujada, ko ku tsokane ni da ayyukan hannuwanku, sa'an nan ba zan hore ku ba.’

7. Duk da haka ba ku kasa kunne gare shi ba, shi Ubangiji ya faɗa, sai kuka tsokane shi da ayyukan hannuwanku. Wannan kuwa zai cuce ku.

8. “Domin haka Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Tun da yake kun ƙi yin biyayya da maganata,

Karanta cikakken babi Irm 25