Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 23:25-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’

26. Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?

27. Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al.

28. Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.

29. Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa.

30. Domin haka, ga shi, ina gāba da annabawan da suke satar maganata daga wurin junansu. Ni Ubangiji na faɗa.

31. Ina kuma gāba da annabawan da suke faɗar ra'ayin kansu, sa'an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya faɗa.’

32. Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”

33. “Kai Irmiya, sa'ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, ‘Mece ce nawayar Ubangiji?’ Sai ka ce masa, ‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,’ ni Ubangiji na faɗa.

34. Idan annabi ko firist, ko wani daga cikin jama'a, ya ce, ‘Nawayar Ubangiji,’ zan hukunta shi duk da iyalin gidansa.

Karanta cikakken babi Irm 23