Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 23:24-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. “Mutum ya iya ɓoye kansa a wanilunguInda ba zan iya ganinsa ba?” In jiUbangiji.“Ashe, ban cika sammai da duniyaba?

25. Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’

26. Har yaushe ƙarya za ta fita daga zuciyar annabawan nan masu annabcin ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗin da yake a zuciyarsu?

27. Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al.

28. Bari annabin da yake da mafarki ya faɗi mafarkinsa, amma wanda yake da maganata ya faɗe ta da aminci. Me ya haɗa ciyawa da alkama? Ni Ubangiji na faɗa.

29. Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa.

30. Domin haka, ga shi, ina gāba da annabawan da suke satar maganata daga wurin junansu. Ni Ubangiji na faɗa.

31. Ina kuma gāba da annabawan da suke faɗar ra'ayin kansu, sa'an nan su ce, ‘Ubangiji ne ya faɗa.’

Karanta cikakken babi Irm 23