Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 22:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.

12. Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.

13. Kaiton wanda ya gina gidansa tahanyar rashin adalci,Benayensa kuma ta hanyar rashingaskiya.Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yimasa aiki a banza,Bai ba shi hakkinsa ba.

14. Kaiton wanda ya ce,“Zan gina wa kaina babban gidaDa waɗansu irin benayemusamman.”Ya yi masa tagogi,Ya manna masa itacen al'ul,Sa'an nan ya yi masa jan shafe.

15. Kana tsammani kai sarki ne,Da yake ƙasarka ta itacen al'ulce?Amma ubanka ya ci, ya sha,Ya yi gaskiya, ya aikata adalci,Ya kuwa zauna lafiya.

16. Ya biya wa matalauta da masubukata hakkinsu,Ya kuwa yi kyau.Abin da ake nufi da sanina ke nan,In ji Ubangiji.

17. Amma ka sa idonka da zuciyarka gaƙazamar riba,Da zubar da jinin marar laifi,Da yin zalunci da danniya.

Karanta cikakken babi Irm 22