Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 22:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Haka Ubangiji ya faɗa, “Ka tafi ka gangara zuwa gidan Sarkin Yahuza, ka faɗi wannan magana a can,

2. ka ce, ‘Ka ji maganar Ubangiji, ya Sarkin Yahuza, kai da kake zaune kan gadon sarautar Dawuda kai da barorinka, da mutanenka waɗanda suke shiga ta ƙofofin nan.

3. Haka Ubangiji ya ce, ka yi gaskiya da adalci, ka ceci wanda ake masa ƙwace daga hannun mai zaluntarsa. Kada ka cuci baƙo, ko maraya, ko gwauruwa, wato matar da mijinta ya rasu, kada kuma ka zubar da jinin marasa laifi a wannan wuri.

4. Hakika idan ka kiyaye wannan magana, sa'an nan sarakunan da za su zauna a kan gadon sarautar Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan gida da karusai da dawakai, su da barorinsu da jama'arsu.

5. Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,’ in ji Ubangiji, ‘wannan fāda ta zama kufai.’ ”

6. Abin da Ubangiji ya ce ke nan a kan fādar Sarkin Yahuza,“Kyanta kamar Gileyad take a gareni,Kamar kuma ƙwanƙolin Lebanon.Duk da haka zan maishe ta hamada,Birnin da ba kowa ciki.

7. Zan shirya waɗanda za su hallakata.Kowannensu da makamansa,Za su sassare zaɓaɓɓun itatuwanal'ul ɗinta, a jefa su a wuta.

8. “Al'ummai masu yawa za su wuce ta gefen wannan birni, kowane mutum zai ce wa maƙwabcinsa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan babban birni?’

9. Za su amsa, su ce, ‘Domin sun keta alkawarin Ubangiji Allahnsu, suka yi sujada ga gumaka, suka bauta musu.’ ”

10. Ku mutanen Yahuza, kada ku yikuka saboda sarki Yosiya,Kada ku yi makokin rasuwarsa,Amma ku yi kuka ƙwarai sabodaɗansa Yehowahaz.Sun ɗauke shi, sun tafi da shi, ba zaiƙara komowa ba,Ba kuma zai ƙara ganin ƙasar daaka haife shi ba.

11. Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.

12. Amma a wurin da suka kai shi zaman talala, a can zai mutu, ba zai ƙara ganin wannan ƙasa ba.

13. Kaiton wanda ya gina gidansa tahanyar rashin adalci,Benayensa kuma ta hanyar rashingaskiya.Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yimasa aiki a banza,Bai ba shi hakkinsa ba.

Karanta cikakken babi Irm 22