Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 19:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Za ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya ku sarakunan Yahuza da mazaunan Urushalima, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, zan kawo wata irin masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.

4. Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.

5. Sun gina wa Ba'al masujadai don su miƙa masa 'ya'yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba.

6. Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa.

7. A wannan wuri zan wofinta dabarun Yahuza da na Urushalima, zan sa a kashe jama'arsu da takobi, a gaban abokan gābansu, ta hannun waɗanda suke neman ransu. Zan ba da gawawwakinsu su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.

Karanta cikakken babi Irm 19