Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 19:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. “Sa'an nan sai ka fasa tulun a gaban mutanen da suka tafi tare da kai,

11. ka kuwa ce musu, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, haka zai farfasa jama'a, da wannan birni kamar yadda aka fashe tulun maginin tukwanen, ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne mutane a Tofet domin za a rasa makabartar da za a binne su.

12. Haka zai yi wa wurin nan da mazauna cikinsa, ya mai da birnin nan kamar Tofet.

13. Gidajen Urushalima da gidajen sarakunan Yahuza da dukan gidaje waɗanda a kan rufinsu aka ƙona wa rundunar sararin sama turare, aka zuba wa gumaka hadayu na sha, za su ƙazantu kamar Tofet.’ ”

14. Sa'an nan Irmiya ya komo daga Tofet, inda Ubangiji ya aike shi don ya yi annabci, sai ya tsaya a fili na Haikalin Ubangiji, ya ce wa dukan jama'a,

15. “Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”

Karanta cikakken babi Irm 19