Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 19:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya ce mini, “Tafi ka sayo tulu a wurin maginin tukwane. Sa'an nan kuma ka ɗauki waɗansu daga cikin dattawan jama'a, da waɗansu manyan firistoci,

2. ku tafi kwarin ɗan Hinnom na mashigin Ƙofar Kasko, ka yi shelar maganar da zan faɗa maka a can.

3. Za ka ce, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ya ku sarakunan Yahuza da mazaunan Urushalima, Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, zan kawo wata irin masifa a wannan wuri, wanda duk ya ji, kunnuwansa za su kaɗa.

4. Ga shi, mutanen nan sun rabu da ni, sun ƙazantar da wannan wuri sun ƙona wa gumaka turare, waɗanda su, ko kakanninsu, ko sarakunan Yahuza, ba su san su ba. Sun cika wannan wuri da jinin marasa laifi.

5. Sun gina wa Ba'al masujadai don su miƙa masa 'ya'yansu maza hadayar ƙonawa, abin da ban umarta ba, ban kuma ba da izni ba, ban ma yi tunanin haka ba.

6. Saboda haka rana tana zuwa da ba za a ƙara ce da wannan wuri Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a ce da shi Kwarin Kisa.

Karanta cikakken babi Irm 19