Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Irm 18:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Irmiya ya ce,

2. “Ka tashi, ka gangara zuwa gidan maginin tukwane, a can zan yi maka magana.”

3. Sai na gangara zuwa gidan maginin tukwanen, na iske shi yana ginin tukwane a kan na'urar ginin tukwanen.

4. Abin da yake ginawa ya lalace a hannunsa, sai ya sāke gina wani abu dabam da yumɓu ɗin, yadda ya ga dama.

5. Sa'an nan Ubangiji ya ce mini,

6. “Ya jama'ar Isra'ila, ashe, ba zan yi da ku kamar yadda maginin tukwanen nan ya yi ba? Duba, kamar yadda yumɓu yake a hannun maginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya ku jama'ar Isra'ila.

7. A duk lokacin da na ce zan tumɓuke, in kakkarya in hallaka wata al'umma, ko wani mulki,

8. idan wannan al'umma da na yi magana a kanta, ta juyo, ta tuba daga mugayen ayyukanta, zan janye masifar da na yi niyyar aukar mata.

9. A duk kuma lokacin da na ce zan gina, in kafa wata al'umma, ko wani mulki,

10. amma idan al'ummar ta aikata mugunta a gabana, ta ƙi saurarawa ga maganar, zan janye alherin da na yi niyyar yi mata.

11. Saboda haka yanzu, sai ka faɗa wa jama'ar Yahuza da mazaunan Urushalima, ka ce, haka Ubangiji ya faɗa, ‘Ga shi, na shirya muku masifa, ina tsara wahalar da za ta same ku. Bari kowannenku ya koma ya bar muguwar hanyarsa, ya gyara al'amuransa da ayyukansa.’

12. Amma za su ce, ‘Wannan ba abin da za mu kula da shi ba ne, mu ra'ayinmu za mu bi, kowannenmu kuwa zai yi bisa ga nufin tattaurar muguwar zuciyarsa.’

13. “Domin haka ni Ubangiji na ce,‘Ka tambayi sauran al'umma.Wa ya taɓa jin irin wannan?Budurwa Isra'ila, ta yi mugun abuƙwarai!

14. Dusar ƙanƙara mai danshi ta taɓarabuwa da tsaunukan Lebanon?Ko ruwan rafuffuka mai sanyi na kandutse ya taɓa ƙonawa?

Karanta cikakken babi Irm 18